Jam’iyyar PDP ta Lashe Zaɓe a Jigawa ta Tsakiya

PDP PDP 1
PDP PDP 1

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana Alhaji Habib Mustapha na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar majalisar dattawa ta Santoriyar Jigawa ta tsakiya.

Jami’in dake tattara sakamakon zaɓe, Farfesa Usman Haruna, wanda ya bayyana sakamakon zaben ranar Litinin a Dutse, ya ce Mustapha ya samu kuri’u dubu 153 da 731 kuri’un da suka sanya ya yi nasara.

Farfesa Haruna ya ce Sanata Sabo Nakudu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 134 da 802 inda ya kasance na biyu.

Ya ƙara da cewa Honorable Musa Bako na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u dubu 18 da 662, yayin da Malam Musa Abdullahi na Jam’iyyar ADC ya samu kuri’u 620.

Jam’in tattara sakamakon zaɓen ya kuma ce Hajiya Hindatu Ibrahim ta Jam’iyyar NRM ta samu kuri’u 462, yayin da Gambo Bala Amina ta SDP ta samu kuri’u 292.

Sanata Sabo Nakudu shi ne mai ci a yanzu kuma ya kasance dan majalisar wakilai wanda ya yi wa’adi biyu a baya kafin zaman sa Sanata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here