Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu da ke Kano (KHAIRUN) ta sake tabbatar da aniyar ta wajen haɓaka nagartar ilimi da ci gaban ƙwararru ta hanyar shirya taron horaswa na yini guda ga dukkan malamanta.
Wannan bayani ya fito ne a wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulɗa da jama’a da tallata jami’ar, Bilal Dahiru Tijjani, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa taron, wanda aka gudanar a ranar Laraba, kwamitin shirya laccoci da tarukan jami’ar ne ya shirya shi ƙarƙashin taken “Muhimman Ayyuka Uku na Malamai: Koyarwa, Kimantawa da Rahotanni.”
An bayyana cewa taron ya kasance don ƙarfafa ingancin koyarwa, inganta dabarun isar da darasi, da kuma tabbatar da bin ƙa’idodin jami’a da ake buƙata daga malamai.
Shugaban jami’ar, Farfesa Abdulrashid Garba, shi ne mai gabatar da taron, inda ya jagoranci mahalarta, wajen tattaunawa mai ma’ana kan rawar da malamai ke takawa wajen tabbatar da sahihancin ilimi da aminci a jami’a.
A yayin bada horon, mahalarta sun koyi hanyoyin koyarwa na zamani, dabarun kimantawa cikin gaskiya, da kuma ingantattun hanyoyin bayar da rahotannin karatu.
Taron ya ƙunshi tattaunawar rukuni-rukuni da musayar kwarewa tsakanin malamai.
Sanarwar ta kammala da cewa wannan taron horaswa wata muhimmiya ce mataki da jami’ar ta ɗauka wajen gina al’umma ta malamai masu ƙwarewa, jajircewa da bin ƙa’ida, waɗanda za su iya samar da ingantaccen ilimi da bincike mai tasiri a matakin duniya.













































