Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB, ta fara gudanar da bincike a kan wasu kura-kurai da ake samu a fannin fasaha, biyo bayan korafe-korafen da aka yi na rashin tabuka komai a jarrabawar UTME ta 2025.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bada shawara kan harkokin yada labarai a Abuja, Dr Fabian Benjamin ya fitar ranar Litinin.
Benjamin ya ce hukumar ta kuma hada kai da mataimakan shugabannin hukumar da kwararrun don tantance tushe da kuma tabbatar da cewa ‘yan takarar da abin ya shafa sun sami warwarewar matsalar da ya dace idan an tabbatar da kurakurai.
Ya kara da cewa hukumar ta damu musamman kan korafe-korafen da ba a saba gani ba da suka samo asali daga wasu jihohi da kuma yin nazari dalla-dalla domin ganowa da warware duk wata matsala ta fasaha.
Dalibai suna Barazanar daukar matakin Shari’a
Shigar hukumar ta JAMB ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa dubban dalibai na shirin shigar da hukumar kara bisa zargin tafka magudi.
Mutane da yawa sun yi iƙirarin sun ci karo da matsaloli na’ura da kuma nunin tambayoyin da ba su dace ba yayin gwajin.
Takaddamar dai ta kai makura bayan da hukumar ta JAMB ta bayyana cewa a cikin kididdigar da ta nuna cewa sama da dalibai miliyan 1.5 daga cikin miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME na bana sun samu kasa da 200 daga cikin 400 da ake iya samu.
Wannan kididdigar ta haifar da damuwa s kasa da hayaniya kafofin sada zumunta.













































