ICPC tana binciken kararraki 100 kan badakalar daukar ma’aikata

ICPC HQ
ICPC HQ

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, ta ce ta samu tare da binciken kusan korafe-korafe 100 kan badakalar daukar ma’aikata daga cibiyoyin da ma’aikatun gwamnati da dama.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye ne ya bayyana haka a wajen taron tattaunawa kan “Kaddamar da gaskiya a tsarin daukar ma’aikatan gwamnati a Najeriya” ranar Talata a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa, Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ACAN), bangaren bincike da horarwa na ICPC ce ta shirya tattaunawar manufofin.

Tattaunawar dai na da nufin samar da wani takaitaccen bayani kan manufofin da za su jagoranci kasar kan batun dakile cin hanci da rashawa da kuma rage yawan kura-kuran da ake samu wajen daukar ma’aikatan gwamnati a Najeriya.
Hakanan ana nufin taimakawa gwamnati don samun adadin da ya dace da ingancin ma’aikatan gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here