Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta kwato wasu motocin gwamnati da ke hannun tsoffin kwamishinoni da suka ƙi mayar da su bayan sun sauka daga muƙamansu.
Da yake zantawa da SolaceBase kan lamarin, shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ya ce an gudanar da aikin ne da safiyar Alhamis bayan umarnin da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya bayar na a mayar da motocin, amma ba a bi ba.
Ya ce matakin ya yi daidai da nauyin da doka ta ɗora wa hukumar na kare dukiyar jama’a.
Ya ƙara da cewa an ba su isasshen lokaci su mayar da motocin da kansu bayan wasiƙar da aka aike musu, amma suka yi watsi da umarnin, wanda hakan ya sa dole aka ɗauki matakin tilasta bin doka.
Shugaban ya ce ba a samu turjiya ba yayin aikin sai a wajen tsohon Kwamishinan Tsaro, Air Vice Marshal Ibrahim Umar (rtd), inda aka ɗan samu jinkiri kafin daga bisani aka kwato motar.
Ya musanta zargin cewa matakin yana da nasaba da siyasa, yana mai cewa aikin ya yi daidai da alhakin da doka ta ba su na kare dukiyar jama’a.
Daga cikin tsoffin kwamishinonin da aka kwato motocinsu har da tsohon Kwamishinan Tsaro, Air Vice Marshal Ibrahim Umar; tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata; tsohon Kwamishinan Harkokin Jin Kai, Dr. Adamu Aliyu Kibiya; Nasiru Sule Garo, tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman; da kuma tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso.
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa za ta ci gaba da sa ido kan yadda ake amfani da dukiyar gwamnati tare da ɗaukar irin wannan mataki a duk inda ya zama dole.













































