Hukumar NERDC ta ziyarci Jami’ar KHAIRUN domin inganta haɗin gwiwa

WhatsApp Image 2025 10 05 at 06.36.25 750x430

Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu (KHAIRUN) da ke Kano ta karɓi baƙuncin babban sakataren hukumar bincike da ci gaban Ilimi ta Najeriya (NERDC), Farfesa Salisu Shehu, wanda ya kai ziyarar aiki domin tattauna batun haɗin gwiwa da cibiyar ilimin.

A cewar wata sanarwa da mai rikon mukamin darakta na sashen hulɗa da jama’a da tallata ayyuka, Bilal Dahiru Tijjani, ya sanyawa hannu a ranar Asabar, ziyarar ta kasance don zurfafa dangantaka da samar da sabbin damar haɗin kai tsakanin hukumar da jami’ar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa yayin ziyarar, Farfesa Shehu ya taya jami’ar murna bisa samun lasisin aiki na dindindin daga hukumar kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), wanda ke tabbatar da sahihancin ayyukan jami’ar da ingancin tsarin ta.

Karin labari: Gasar Hadisi: Matasa shida sun lashe kyaututtuka a gasar da aka shirya a Najeriya

Ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce gina zumunci, ƙarfafa haɗin gwiwa, da gano sabbin hanyoyin haɗa kai tsakanin hukumar da wannan jami’a mai tasowa.

A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar KHAIRUN, Farfesa Abdulrashid Garba, ya bayyana cewa jami’ar a shirye take ta yi aiki tare da hukumar NERDC a fannoni da dama da ke da amfani ga bangarorin biyu.

Farfesa Garba ya ƙara da cewa jami’ar za ta samar da duk wata dama da take da ita domin tallafa wa hukumar wajen shirya taruka, bitoci, ko shirye-shiryen horo, idan akwai buƙata nan gaba.

Ya kuma yabawa hukumar NERDC bisa irin gudunmawar da take bayarwa wajen ƙarfafa tsarin ilimi a Najeriya, tare da ba da shawara kan muhimman batutuwan da suka shafi inganta wannan fanni a matakai daban-daban na ilimi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here