Gasar Hadisi: Matasa shida sun lashe kyaututtuka a gasar da aka shirya a Najeriya

1000207412 750x430

Matasa shida ‘yan Najeriya ne suka bayyana a matsayin zakarun gasar Hadisi da Gidauniyar King Mohammed VI ta Malaman Afrika da ke Maroko ta shirya.

Ɗaya daga cikin alkalai na gasar, Dr. AbdulGaniyu Tijani, ne ya bayyana hakan yayin bikin rufe gasar da aka gudanar a birnin Abuja a ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa a rukuni na farko na gasar, waɗanda suka lashe kyautar su ne Fatima Turbo, Muhammad Ibrahim, da Abubakar Abba, dukkansu daga jihar Borno.

A rukuni na biyu kuwa, akwai Saleh Al-Amin daga Borno, Ahmed Kolawole daga Kwara, da Khalifah Jibril daga Kaduna sune suka fito zakaru.

Kowane rukuni yana da masu nasara uku, inda na farko ya samu Naira dubu 250,000, na biyu suka samu Na’ura 200,000, sannan na uku suka samu 150,000 a matsayin kyauta.

Tijani ya bayyana cewa babban manufar gasar shi ne ƙarfafa matasa wajen koyo da kuma haddace Hadisan Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ba wai don samun kuɗi kawai ba.

Ya ce wannan shi ne zango na biyu na gasar, bayan wanda aka gudanar a bara.

Tijani ya ƙara da cewa, Najeriya ta fi kowace ƙasa a Afirka ƙwarewa wajen haddace Alƙur’ani, amma ba a mai da hankali sosai kan haddace Hadisai ba, don haka wannan gasar za ta ƙarfafa matasa wajen yin hakan.

Ya bayyana cewa gasar na da rukuni uku, inda rukuni na farko ke haddace Hadisai 40 tare da sanadinsu, rukuni na biyu ke haddace 35 tare da fahimtar ma’anonin kalmomi, sannan rukuni na uku ke haddace 25 tare da sanin hukuncin da Hadisan suka ƙunsa.

Karin labari: Ƙungiyar Malamai Ulama ta yi watsi da zargin kisan kiyashi na Kiristoci a Najeriya

Tijani ya ce fiye da ’yan takara 560 ne suka fara gasar, kuma an shafe wata guda ana zaɓen fitattun masu iya jawabi.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka ci gasar za su samu horo da shiri domin halartar gasar matakin Afirka da za ta biyo baya.

A nasa bangaren, Farfesa Ibrahim Maqari, ɗaya daga cikin masu tsara gasar, ya ce za a shirya sansani na musamman domin ba wa zakarun gasar horo kan ɓangarorin da suka nuna rauni kafin gasar Afirka.

Ɗaya daga cikin zakarun, Ahmed Kolawole, ya bayyana cewa gasar ta taimaka masa wajen sanin Hadisai da bai sani ba a baya, tare da ƙarfafa shi wajen bin Sunnah da koyarwar Annabi.

Ya ce, “Na koya abubuwa masu yawa daga gasar nan, musamman kan abin da Hadisai ke koyarwa game da salla da sauran muhimman fannoni na addinin Musulunci.”

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here