Hukumar kula da Gasa da kare haƙƙin masu Saye ta kulle wasu shaguna a Kano yayin sumame da ta kai bisa zargin tauye ma’aunin Tufafi a wasu manyan ma’ajiyoyi da shagunan dillalai da ake zargin suna sayar da yaduddukan da aka yaushe ma’aunin su.
A sumamen hukumar ranar Larabawa da ta gudanar a yankin masana’antu na Sharada da wasu wuraren kasuwanci, inda aka kai samame kan kamfanonin LGR Products, UME Products, Nana Textile Products, Mama Africa Products da UE Products da sauransu.
Daraktar sa ido da bincike a hukumar, Boladale Adeyanka, ta bayyana cewa samamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka tabbatar da su da kuma makonni na sa ido a kasuwa da suka gano munanan dabarun kasuwanci da wasu ‘yan kasuwa ke amfani da shi.
Hukumar ta gano cewa wasu dillalan yadudduka suna sayar da kaya da ba su kai yawan ma’aunin da aka rubuta ba, inda yadudduka masu yawa yadi 10 ake kauye su su zama yadi 9, yayin da wasu masu yawan yadi 5 ake kauye su zuwa yadi 4 da rabi.
Adeyanka ta ce irin wannan aiki ya saba wa tanade-tanaden dokar FCCPA ta 2018, wadda ta haramta sayar da kayayyaki cikin karya ko yaudara game da awo ko ingancin kaya.
Bayan tabbatar da laifin, mataimakin shugaban hukumar, Tunji Bello, ya ba da umarnin kulle shagunan da abin ya shafa domin ci gaba da bincike tare da kwace samfurorin kayan don tantance inganci da tsawon yaduddukan.
Hukumar ta bayyana cewa irin wannan yaudara tana cutar da masu siye da kuma rugujewa kasuwanci mai gaskiya, tana mai nanata cewa manufarta ita ce kare masu amfani da kaya daga munanan dabarun kasuwanci da karya.
Ta kuma shawarci jama’a da su rika kai rahoton duk wani shakku na sayar da kaya cikin yaudara ta hanyoyin korafi na hukuma, tana mai tabbatar da cewa FCCPC za ta ci gaba da amfani da doka wajen dakile irin wannan cin zarafi a kasuwanni.













































