Gwmanatin tarayya ta yi asarar Naira Milyan 113 sakamakon dakatar da sifirin jirgin kasan Abuja-Kaduna – NRC

Train station
Train station

Manajan daraktan hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya Fidet Okhiria, ya ce gwamnatin tarayya ta yi asarar kimanin Naira miliyan 113 sakamakon dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna sama da watanni takwas.

A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Abuja a karahen mako, Mista Okhiria ya ce kamfanin ya tattara wannan adadi ne ta hanyar amfani da takaddun samun kudin shiga tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

“Lokaci na ƙarshe da muka bincika, shine tsakanin watannin Fabrairu da Agusta. Mun yi asarar kusan Naira miliyan 113,” inji shi.

Sai dai ya ce ‘yan Najeriya da dama ma sun tafka asara afakaice sakamakon dakatar da ayyukan hanyar.

“Akwai mutane da suke saye da sayarwa a cikin taahar jirgin, akwai kuma wadanda suka bude shaguna, kuma mutane suna ba su tallafi saboda jiragen suna hada hada.

“Don haka a maimakon mu koma kashe karin kudi don gyara bangarorin dasuka lalace, ya kamata mu yi amfani da su wajen inganta rayuwarmu ta wasu ayyuka don amfanin ‘yan Najeriya,” in ji Mista Okhiria.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here