Taron majalisar zartaswa na tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ya amince da ba da lasisi ga sabbin jami’o’in a kasar nan guda 37.
Hakan na zuwa ne duk kuwa da korafe-korafen da ake tayi gameda yawaitar jami’o’i a Najeriya.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya sanar da hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa.
Adamu ya ce ci gaban ne ya kawo adadin jami’o’in da gwamnatin Buhari ta ba da lasisi zuwa 72 tun daga 2015.
Ko da yake ministan bai ambaci sunayen jami’o’in ba, amma ya bayyana cewa daya daga cikinsu jami’a ce ta yanar gizo, wadda ita ce irinta ta farko a Najeriya, kuma mallakar wata mata ce daga jihar Bauchi, tare da sa ran za ta rika daukar nauyin irin wadannan matan musulmi ‘yan Arewa.
Da yake gabatar da tambayoyi kan fa’idar karin jami’o’i, Adamu ya bayyana cewa masu jami’o’in na da isassun kudaden tafiyar da su, kuma bai kamata a hana su dama ba.
Ministan ya ci gaba da bayanin cewa a zahiri Najeriya na bukatar karin jami’o’i saboda wadanda ake da su ba sa iya kwashe dukkan masu sha’awar neman ilimin shiga jami’o’i.













































