Gwamnatin tarayya da ƙungiyar ASUU na cigaba da tattaunawa domin dakile yajin aiki

ASUU vs Federal Government 1

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da tayin ƙarin albashi na kashi arba’in ga malaman jami’o’i da ke ƙarƙashin ƙungiyar ASUU.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da hakan a Abuja yayin da shugabancin ƙungiyar ke shirin komawa teburin tattaunawa tare da tawagar gwamnati ƙarƙashin jagorancin Yayale Ahmed.

An yanke wannan matsaya ne bayan zaman majalisar zartarwa ta ƙasa ta ƙungiyar da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi, inda shugabannin rassan ƙungiyar za su isar da bayanan ga membobin su a sassan ƙasar nan.

A ƙarshen taron, wani memba ya bayyana cewa ƙungiyar za ta cigaba da tattaunawa da gwamnati mako mai zuwa, bayan an miƙa tayin ƙarin albashi na kashi arba’in da za a tattauna a kan sa.

Wa’adin wata guda da ASUU ta bai wa gwamnati ya ƙare a ranar Asabar, lamarin da ya janyo bukatar zaman a tsakanin al’ummar jami’o’in gwamnati na ƙasar.

A wani yunƙuri na ƙarshe domin dakile yajin aiki, gwamnati ta kira shugabannin ƙungiyar zuwa taro a Abuja a ranar Litinin, wanda zai ci gaba zuwa Talata, sai dai ba a bayyana cikakken bayanin tattaunawar ba saboda ka’idojin tsarin sulhu.

Ƙungiyar ta ce za ta shiga yajin aiki gaba ɗaya bisa dalilin cewa gwamnati na nuna sakaci ga bukatunta, musamman batun sabunta yarjejeniyar shekarar 2009, biyan albashi da alawus ɗin da ake binsu, da kuma kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i da ake jira.

Ministan ilimi Dr. Tunji Alausa, wanda yake ƙasar waje, ya ce gwamnati ta cika bukatun ƙungiyar, yana jaddada umarnin Shugaba Bola Tinubu na cewa kar a samu yajin aiki a jami’o’in gwamnati, tare da cigaba da tattaunawa domin tabbatar da ɗalibai sun kasance a makarantu.

Ya ce gwamnati na ƙoƙari matuƙa don tabbatar da zaman lafiya a jami’o’i, yana mai nuni da cewa an yi nisa wajen warware matsalolin da suka haifar da barazanar yajin aiki da ƙungiyar ta yi.

A nata bangaren, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta nuna cikakken goyon baya ga ASUU, har ma a cewar ta za ta kare muradun al’ummar jami’o’i idan gwamnati ta gaza aiwatar da bukatun da ake nema.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here