Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da kudirinta na dawowa da kuma kare gadon tarihi da al’adun gargajiya na jihar, waɗanda da dama suka salwanta sakamakon faɗaɗa birni da sakaci a tsawon shekaru.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin liyafar da aka shirya wa shirin Shirin Ƙungiyar Masu Aikin Sa-kai na Gado ta Duniya wato “World Heritage Volunteers Initiative”, inda ya bayyana shirin a matsayin abin yabo da zai taimaka wajen farfaɗo da tarihin Kano da ɗaukaka gadonta.
Wakilin gwamnan, sakataren gwamnatin jihar Umar Ibrahim, ya bayyana cewa gwamnati na goyon bayan shirin sosai, tare da tabbatar da cewa za ta ba da duk wata gudunmawa da ake buƙata domin cimma nasara.
Gwamna Yusuf ya nuna damuwarsa kan yadda aka rasa muhimman kayan tarihi da gine-ginen tarihi da ke nuna asali, yana mai cewa hakan babban abin takaici ne da ya kamata a gyara cikin gaggawa.
Ya ce wasu muhimman wuraren tarihi, kamar tsofaffin ɗakunan taron birnin Kano, sun lalace saboda ayyukan kasuwanci da ci gaban zamani.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta himmatu wajen dawo da abin da ya rage daga waɗannan kayayyakin tarihi tare da tabbatar da cewa al’ummar gaba za su fahimci muhimmancinsu da tarihin Kano.
A nata jawabin, shugabar gidauniyar shirya bukukuwan tarihi a Afrika “African International Documentary Festival Foundation (AFIDFF)” Malame Mangdza, ta bayyana cewa suna da niyyar ci gaba da karewa da kuma inganta wuraren tarihi da abin tunawa a nahiyar Afrika, yayin da Kano ke karɓar baƙuncin gangamin nuna kayan tarihi “Heritage Campaign” na shekarar 2025.
Mangdza ta ce Kano ta samu damar zama ɗaya daga cikin jihohin da ke karɓar wannan shiri ne saboda tarihinta mai ɗorewa da al’adunta masu ban mamaki da kuma gadon da ta gada tun fil azal.
Ta kuma bayyana cewa shirin zai haɗa da al’ummomi na cikin gida, masarautu, hukumomin gwamnati da masana wajen tattara tarihin Kano da wuraren tunawarta, domin tallafa wa ƙoƙarin kare gadon tarihi a faɗin Afrika.
A nasa jawabin, wakilin Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) daga Abuja, Abdullah Muhammad, ya yaba wa Gwamnatin Kano bisa kwazon da take nunawa wajen dawo da gine-ginen tarihi da kuma kare martabar al’adunta, yana mai cewa abin da suka gani a Kano ya bambanta da sauran wurare da suka ziyarta a nahiyar Afrika.












































