Jami’ar Stanford ta Amurka tare da kamfanin buga binciken kimiyya na duniya Elsevier sun saka sunayen malamai uku daga jami’ar Bayero Kano cikin jerin kashi biyu cikin ɗari na fitattun masana kimiyya mafi tasiri a duniya na shekarar 2025.
Wannan rahoto da aka gina bisa bayanan cibiyar Scopus ya nuna masana da bincikensu ke samun yawan ambato a cikin muƙaloli na duniya.
An yi amfani da ma’auni irin su adadin ambato gaba ɗaya, ƙididdigar h-index, ƙididdigar haɗin gwiwa (hm-index), da haɗaɗɗen alamar tasiri (c-score) wajen tantance ƙwarewa da tasirin bincike a fannonin kimiyya 22 da ƙananan rassa 174.
Malamai uku daga jami’ar Bayero Kano da suka samu wannan matsayi sun haɗa da Farfesa Abdulrazaq Garba Habib daga sashen Internal Medicine wanda ya zo na 82 a fannin maganin ƙwayoyin cututtuka; yana da ƙididdigar h-index 11 da hm-index 5.
Na biyu shi ne Dakta Sunusi Marwana Maniadan daga sashen injiniyan kere-kere, wanda ya zo na 4,131 a fannin fasahohin kayan aiki, yana da h-index 14 da hm-index 4, sai na uku kuma shi ne Dakta Isah Baba Abdullahi daga sashen kimiyyar lissafi, wanda ya zo na 142 a fannin lissafin taurari, yana da h-index 8 da hm-index 4.
Wannan jerin da jami’ar Stanford tare da Elsevier suka fitar ana ɗaukar shi a matsayin ɗaya daga cikin mafi sahihanci wajen tantance masu tasiri a harkar binciken kimiyya, kuma yana jaddada irin girmamawar da binciken malamai daga Najeriya ke samu a fagen duniya.
Shugaban jami’ar Bayero Kano, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana wannan nasara a matsayin shaida ta girman cigaban jami’ar a fannin bincike da tasirin karatunta a matakin ƙasa da ƙetare.
Shigar wadannan malamai uku cikin jerin masana kimiyya na duniya ya sanya jami’ar Bayero Kano cikin ƙalilan daga cikin jami’o’in Najeriya da ke da wakilci fiye da ɗaya a irin wannan lissafi na ƙasa da ƙasa.












































