
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin tunawa da farkon sabuwar kalandar Musulunci ta 1446 bayan hijira.
Ya kuma hori jama’a da su yi amfani da hutun wajen yin tunani a kan shekarar da ta gabata tare da sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukan da za su amfanar da juna da za su haifar da nasara ga al’umma a wannan mawuyacin lokaci da wahala.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye ya fitar ranar Juma’a.
Karin labari: “Gwamnatin tarayya za ta karawa masu hidimar kasa albashi” – Darakta Janar
A nata bangaren, gwamnati za ta ci gaba da bujuro da tsare-tsare da za su ba mutane damar dogaro da kai.
Gwamnan ya bukaci al’ummar Musulmi da su kara kaimi wajen addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a Jihar.
Ya kuma bayyana fatansa tare da addu’o’i da goyon bayan al’umma, gwamnatinsa za ta juyar da dukiyoyin jihar tare da mayar da ita jihar da ta fi samun ci gaban tattalin arziki a tsakanin takwarorinta na kasa.












































