Gwamnatin jihar Lagos ta bayar da umarnin yin bincike kan mutuwar wasu tagwaye bayan an yi musu rigakafi

ezgif 5daf7c72c95c558d 300x200 1

Gwamnatin Jihar Lagos ta bayar da umarnin gudanar da binciken bayan mutuwar tagwaye masu watanni tara, Testimony da Timothy Alozie, waɗanda suka rasu kimanin sa’o’i ashirin da huɗu bayan karɓar rigakafin yau da kullum a wata cibiyar kula da lafiya ta matakin farko a jihar.

Lamarin ya ja hankalin jama’a ne bayan mahaifin yaran, Samuel Alozie wanda aka fi sani da Promise Samuel a TikTok, ya wallafa bidiyo a kafafen sada zumunta yana nuna gawarwakin ‘ya’yansa biyu cikin jakunkunan gawa, tare da bayanin yadda suka mutu jim kaɗan bayan karɓar allurar rigakafin.

Mahaifin yaran ya kai su cibiyar lafiya domin karɓar rigakafin yau da kullum da safe, inda bayan an yi musu allura nan take suka fara nuna matsanancin ciwo.

Ya bayyana cewa daga wannan lokaci yaran suka kasa cin abinci, suka daina wasa, kuma ba su nuna kuzarin da suka saba ba.

Ma’aikaciyar jinya a cibiyar lafiyar ta shawarci iyayen da su ba yaran maganin paracetamol idan jikin su ya yi zafi.

Iyayen sun bi wannan shawara tare da yi musu wanka da ruwan sanyi, amma lafiyar yaran ba ta samu ba, lamarin da ya kai ga rasuwarsu da safe washegari a lokaci guda.

Mahaifin ya nuna cewa yaran suna cikin cikakkiyar lafiya kafin karɓar rigakafin, kuma tun daga haihuwarsu yana tabbatar da cewa suna karɓar dukkan rigakafin da aka tanada musu.

Ya kuma lura cewa ma’aikaciyar jinyar da ta yi musu allurar ƙarshe ba ita ce wadda ta saba kula da yaransa a baya ba.

Ya ƙi yarda da bayanin farko da aka bayar daga cibiyar lafiyar wanda ya danganta mutuwar yaran da cutar da ke fitowa daga abinci, yana mai bayyana cewa irin abincin da ake basu tun suna ƙanana bai taɓa jawo musu wata matsala ba.

A halin da ake ciki, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Lagos, Dakta Ibrahim Mustafa, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike tare da umarnin yin gwaje gwaje bayan mutuwarsu.

Ya bayyana cewa an kai gawarwakin yaran dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Lagos, kuma gwamnati za ta fitar da sakamakon binciken ga jama’a da zarar an kammala.

Sai dai mahaifin yaran ya nuna fargabar cewa sakamakon binciken na iya karkata ne domin kare cibiyar lafiyar mallakin gwamnati, inda ya yi kira ga lauyoyi da masu kare haƙƙin ɗan adam da su taimaka masa domin neman adalci ga ‘ya’yansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here