Gwamnatin jihar Kano ta hana aikin Adaidata Sahu bayan karfe 10 na dare

Tricycle arrest
Tricycle arrest

Gwamnatin jihar Kano ta hana yin aikin adaidata Sahu bayan karfe goma na dare, dokar kuma zata fara aiki ne daga ranar Alhamis na wannan watan da muke ciki.

Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar yau Litinin.

Sanarwar ta ce an dau matakin ne don magance matsalar tsaro da jihar Kano ke fama da ita

Ya kuma yi kira ga masu tuka adaidai ta shahu da su bi dokar da gwamnatin ta kafa, don gujewa fushin hukuma.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here