An yi asarar kaya na miliyoyin naira a sakamakon gobara da ta tashi a kasuwar sayar da kayan mota ta Akere da ke Ajegunle a Apapa, da ke jihar Lagos.
Haka kuma an samu gawar wani mai gadi mai shekara 65, a kusa da inda gobarar ta tashi kamar yadda bayanai suka nuna.
A wata sanarwa da darektar hukumar kashe gobara ta jihar Legas Adeseye Margaret, ta fitar a yau Laraba ta ce, gobarar ta tashi ne da wajen ƙarfe 3:30 na dare.
Shugaban ta kara da cewa sai an gudanar da cikakken bincike za a san dailin tashin gobarar da yawan shaguna da dukiyar da ta ɓannata.
Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Benjamin Hundeyin ya tabbatar mata cewa mai gadin da aka tsinci gawarsa a kasuwar harbinsa aka yi.
Kakakin ya ce an gane gawar ta wani mai gadi ce a kasuwar kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.










































