Gidauniyar Barau ta tantance ɗalibai 215 don ba su tallafin karatu a gida na shekarar 2025

barau 1 666x430

Gidauniyar Barau I. Jibrin (BIJF) ta fitar da sunayen dalibai 215 don neman gurbin karatu na gida a matakin Digiri na biyu don tallafawa Ilimi na 2025/2026.

Sanata Barau, a kokarinsa na fadada hanyoyin samun ilimi ga matasan Najeriya, ya kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu na kasashen waje da na cikin gida, inda dalibai saba’in a halin yanzu suke ci gaba da karatun digiri a Indiya.

Wata sanarwa da mataimakin shugaban majalisar dattijai na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce ana gayyatar wadanda aka zaba don shiga cikin shirye-shiryen karatun digiri na biyu na cikin gida domin tattaunawa da tantance su a ranakun 20 zuwa 21 ga Afrilu 2025 a Jami’ar Bayero, a sashin ci gaba da karatu na Education (SCE) da ke Goron Dutse, Kwanar Taya a Kano.

Idan za a iya tunawa cewa a ranar 6 ga watan Janairun wannan shekara ne gidauniyar Barau I Jibrin ta bude shafin neman gurbin karatu a gida, inda aka zabo wadanda suka cancanta daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Karin karatu: Jami’ar KHAIRUN ta yi bikin rantsar da sabbin dalibai sama da 570

“Shirye-shiryen sun hada da M.Sc. Artificial Intelligence, M.Sc. Robotics Technology, M.Sc. Cyber Security, M.Sc. Data Science, M.Sc. Information Technology, M.Sc. Software Development, M.Sc. Mineral Exploration, M.Sc. Hydrogeology & Environmental Geology, M.Sc. Oil and Gas Operations, M.Sc. Applied Geophysics, M.Sc. Metallurgical and Material Engineering, M.Sc. Climate Change Management, M.Eng. Mechatronic and M.Eng. Intelligence System,” kamar yadda gidauniyar ta bayyana.

SolaceBase ta ruwaito cewa an zabi jami’o’i shida, ciki har da Jami’ar Bayero Kano, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Jami’ar Ibadan, Jami’ar Legas, Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife da Jami’ar Nsukka ta Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here