Fadar shugaban ƙasa ta musanta sabon rahoton tattalin arziƙi da babban mai bayar da lamuni na ƙasa da ƙasa, wato Bankin Duniya, ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 a Najeriya na rayuwa cikin talauci.
Fadar gwamnatin ta bayyana wannan ƙididdiga a matsayin wacce ba ta dace da ainihin halin tattalin arziƙin ƙasar ba.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da hulɗar jama’a, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa wannan ƙididdiga ta Bankin Duniya dole ne a fassara ta ne bisa iyakokin da tsarin auna talauci na duniya ya tanada.
A cewar sa, ba ta nuna ainihin adadin talakawan ƙasar ba.
Fadar gwamnatin ta bayyana cewa adadin talakawa miliyan 139 an samo shi ne daga ma’aunin duniya na talauci wanda ke kimanta kowane mutum da kuɗin da bai wuce dala biyu da ƙarin kwata a rana ba, wanda aka kafa tun a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai bisa tsarin da ake kira daidaiton ƙarfin saye (Purchasing Power Parity). Ta ce idan aka fassara wannan adadi da kuɗin Najeriya na yau, zai haura naira dubu ɗari a wata, wanda ya fi sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasar da yake naira dubu saba’in.
Gwamnatin ta gargadi al’umma da kada su ɗauki wannan ƙididdiga a matsayin adadin zahirin talakawa a ƙasar, saboda ma’aunin da Bankin Duniya ke amfani da shi yana dogara ne da tsoffin bayanan amfani da kayan masarufi da aka tattara tun a shekarar dubu biyu da goma sha tara, wanda bai haɗa da tattalin arziƙin bayan fage da kuma tsarin amfanin kai tsaye da ke tallafa wa miliyoyin mutane a Najeriya ba.
Ta ce a maimakon haka, abin da ya fi muhimmanci shi ne hanyar da tattalin arziƙin ƙasar ke bi, wanda yanzu ya koma kan hanya ta murmurewa da sauye-sauyen da ke nufin samar da ci gaban kowa da kowa.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana wasu muhimman shirye-shiryen tallafi da gwamnati ta faɗaɗa, ciki har da shirin ba da tallafin kuɗi ga talakawa wanda ya kai ga iyalai miliyan goma sha biyar a fadin ƙasar, tare da tantance su ta cikin Rajistar Jama’a ta Ƙasa.
Har ila yau, an rarraba fiye da naira biliyan dari biyu da casa’in da bakwai tun daga shekarar dubu biyu da ashirin da uku ga iyalai marasa galihu.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta kafa shirin ci gaban Gundumomi karkashin shirin Sabon Fata, wanda ke aiki a gundumomi dubu takwas da dari takwas da tara da dogo tara, domin samar da ƙananan ayyuka, tallafin rayuwa da kuma hidimomin jama’a kai tsaye ga al’umma.
Sauran shirye-shiryen sun haɗa da Shirin Kula da Jama’a na Ƙasa, wanda ya ƙunshi sassa irin su Shirin Ƙarfafa Matasa da Mata yan Kasuwa, Shirin Lamuni ga ’Yan Kasuwa da Manoma, da kuma Shirin Ciyar da Ɗalibai a Makarantu, waɗanda ke da nufin kare ayyukan yi, ƙarfafa ƙanana da matsakaitan sana’o’i, da kuma tabbatar da cewa yara suna cigaba da zuwa makaranta.
Gwamnatin ta kuma kafa Kudin Ci gaban Ayyuka na Sabon Fata, domin saka jari a sassan wutar lantarki, hanyoyi, da gidaje, tare da kafa Kamfanin Kula da Lamuni na Ƙasa domin bai wa ƙanana masana’antu, matasa da mata damar samun rance mai sauƙi ta hanyar haɗin gwiwa da bankuna.
Fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnati na aiki tukuru wajen magance matsalolin da suka daɗe suna hana ci gaban ƙasa, kamar cire tallafin mai da kuma daidaita tsarin musayar kuɗi, wanda ta bayyana a matsayin matakai masu ciwo amma dole don farfaɗo da tattalin arziƙi.
Fadar shugaban ƙasa ta ce burin gwamnati a nan gaba shi ne ganin wannan daidaituwa na tattalin arziƙi ya fassaru zuwa sauƙin rayuwa ga talakawa ta fuskar farashin abinci, samun ayyukan yi, da kuma ingantattun ababen more rayuwa.
A ƙarshe, gwamnatin ta bayyana cewa ’yan ƙasa za su fara jin sauƙi a farashin kayan masarufi da ƙarfin saye yayin da waɗannan shirye-shirye ke kai wa matakin ƙarshe.













































