Dakunan Gwaje-Gwajen Wankin Zuciya Guda Biyu A Najeriya – Salisu Na’inna Dambatta

IMG 20230813 WA0138 750x430 (1)
IMG 20230813 WA0138 750x430 (1)

Wani rahoto da jaridar dake bibiyar likitancin zuciya wato Nigerian Journal of Cardiology ta fitar a shekarar 2021 ya nuna cewa, cututtukan zuciya da jijiyoyin jini da suka shafi zuciya musamman hawan jini da ke haifar da kiba, na kara kamari a tsakanin matasa a kasar.

Likitocin dasuka kware a fannin lafiyar zuciya, wadanda suka hada da hauhawar jini da bugun zuciya na bukatar muhimman kayan aiki na musamman don kula da majinyatan su cikin lokaci.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suke buƙata cikin gaggawa shine dakunan gwaje gwaje, tiyata da wankin zuwa wato (Cath Lab) a takaice.

Farfesa Kamilu Musa Karaye, Farfesa a fannin likitanci kuma mai ba da shawara ga likitocin zuciya a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Farfesa Kamilu Musa Karaye ya nuna cewa, dakunan gwaje-gwajen wankin zuciya, cibiyoyi ne na musamman na fasahar likitanci da ake amfani da su don tantancewa da kuma magance cututtukan zuciya.

Hakanan za’a iya amfani da kayan aikin da ke cikin dakunan gwaje-gwajen zuciya a hanyoyi daban-daban dasuka hadar da faɗaɗawa, kunkuntar ko toshewar hanyoyin jini.

Dakin gwaje-gwaje na kuma baiwa likitocin tiyata damar gudanar da gwaje-gwaje da hanyoyi masu yawa a cikin bincike da kuma kula da cututtukan zuciya da suka shafi zuciya da jijiyoyin jini.”

Akwai dakunan gwaje-gwaje biyu kacal, daya a wani asibiti mai zaman kansa a Legas, dayan kuma a asibitin fadar gwamnati da ke Abuja.

Dukkansu a bayyane take ba sa iya gamsar da al’ummar ƙasar ba. Mai yiwuwa ba zai iya isa ga yawancin marasa lafiya dake fama da cututtukan zuciya da jijiyoyin jinin ba. Ko kuma jqmaa da dama ba su da kuɗin da za yi musu aikin.

Dayan kuma a asibitin faadar shugaban kasa, an tanadar da shi ne don yin hidima ga manyan shugabannin siyasar ƙasar.

Bayanai daga majiyoyi daban-daban na nuni da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fama da yawan mace-mace sakamakon cututtukan zuciya. Farfesa Kamilu Musa Karaye, farfesa a fannin likitanci kuma mai ba da shawara kan harkokin kafofin watsa labarai da ke koyarwa da kuma gudanar da bincike a jami’ar Bayero Kano, da kuma asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya bayyana cewa jihar Kano na daya daga cikin jihihi da suka fi kamuwa da cututtukan zuciya.

An gudanar da tiyatar zuciya ta farko mai sarƙaƙiya a cikin 1974, shaidar kasancewar kwararrun likitocin zuciya da ma’aikatan da ke da alaƙa don sanya ta zama aiki na yau da kullum.

Wani abin mamaki shi ne cewa babu daya daga cikin asibitocin koyarwa na jami’o’i 22, da cibiyoyin kulada kiwon lafiya na tarayya 20 da kuma asibitocin kwararru 17 da ke kasar nan da ke da dakin gwaje-gwajen tiyatar zuciya karakakaf.

Duk da cewa Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke kula da dimbin al’umma da kuma wasu asibitocin koyarwa na gwamnatin tarayya suna bakin kokarinsu wajen ganin an samu kowannensu, amma a halin yanzu ana matukar ganin an samar dasu a wadace.

Abin mamaki kuma shine farashin kudin aikin yana farawa ne daga $ 200,000 don mafi mahimmanci tare da ƴan kayan aiki zuwa Dala Milyan $3- $ 6 na aikin yau da kullun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here