Rufe iyakokin Nijar: Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Arewa ta koka Kan Tafka Asarar Bilyoyin Nerori.

Truck for Niger (1)
Truck for Niger (1)

Kungiyar Raya Tattalin Arziki ta Arewa (AED) ta bayyana cewa asarar makudan kudade da aka samu sakamakon rufe iyakokin Nijar da Najeriya ya kai Naira biliyan 13 a duk mako.

Taron wanda aka yi da manema labarai a Abuja a karshen mako, kungiyar ta kuma koka kan yadda ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya ke da kwantenoni fiye da 2000 da suka makale sakamakon rufewar da aka yi sakamakon juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Da yakewa manema labarai karin haske kan tasirin tattalin arzikin da shawarwarin da aka dauka kawo yanzu, shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Shehu Dandakata ya ce.

“Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2022, cinikin da aka yi tsakanin kasashen biyu ya kai dala miliyan 234 (N171bn) yayin da cinikin da ba na yau da kullun ba ya kai dala miliyan 683, galibi na kayayyaki masu lalacewa.

Dandakata ya kuma lura da cewa: “Al’ummar Nijar sun kai kimanin miliyan 25. Kusan kashi 70% na mutanen suna zaune ne a garuruwan da ke da kusanci da Najeriya.

“’Yan Nijar sun dogara ne da Najeriya don yawancin kayayyakin masarufi da suke amfani da su. Har ila yau, ‘yan kasuwan Najeriya sun dogara ne kan hanyoyin jigilar kayayyaki da ake shigo da su daga Jamhuriyar Nijar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here