NEMA Ta Zayyano Jihohin Najeriya 19 Da Za Su Fuskanci Kalubalen Ambaliyar Ruwa Kwanannan 

flood in yobe.jpeg
flood in yobe.jpeg

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta bayyana cewa aƙalla jihohin Najeriya 19 ne za su fuskanci mamakon ruwan sama da zai iya janyo musu ambaliyar ruwa. Kodinetan hukumar na jihar Legas, Ibrahim Farinloye ne ya bayyana hakan ranar Litinin.

Jihohin da Mista Farinloye ya lissafo da za su fuskanci ambaliyar ruwan saman sun haɗa da Delta, Ekiti, Ondo, Legas, Anambra, Ogun da jihar Nasarawa.

Karin jihohin da aka bayyana za su fuskanci ambaliyar ruwan su ne Kuros Riba, Bauchi, Jigawa, Osun da kuma jihar Kwara. Sauran jihohin Najeriya da Farinloye ya ambata sunansu su ne Zamfara, Sokoto, Adamawa, Taraba, Benuwai, Imo, da kuma jihar Abia.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here