Da gaggawa: ƙasar China ta gargadi Amurka kan tsoma baki cikin harkokin Najeriya bisa zargin yiwa Kiristoci kisan kiyashi

Tinubu Trump (1)

Gwamnatin ƙasar China ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Najeriya, tana mai cewa tana tare da ita wajen jagorantar al’ummarta bisa tafarkin ci gaba da ya dace da halin ƙasar.

A taron manema labarai da aka gudanar a birnin Beijing a yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Mao Ning, ta bayyana cewa “a matsayinta na abokiyar hulɗa ta dabarun ci gaba da Najeriya, ƙasar China tana adawa da kowace ƙasa da ke amfani da addini ko kare haƙƙin ɗan adam a matsayin hujjar tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata ƙasa, ko kuma yin barazanar sanya takunkumi da amfani da ƙarfin soja.”

Wannan magana ta fito ne a yayin da take mayar da martani kan barazanar shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na ɗaukar matakin farwa Najeriya bisa zargin gallazawa Kiristoci.

Mai magana da yawun ƙasar ta kuma bayyana matsayar China kan wani rahoto da ke cewa shugaban ƙasar Venezuela Nicolás Maduro na neman taimakon kayan yaƙi daga ƙasashen China, Rasha da Iran domin shirin kare ƙasarsa daga yiwuwar harin Amurka.

Ta ce ƙasar China tana goyon bayan ƙoƙarin yaƙi da manyan laifukan ƙetare iyaka ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe, amma tana adawa da amfani da ƙarfin soja ko yin barazana da shi wajen hulɗar ƙasashen duniya, tana mai cewa hakan yana kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Latin Amurka da yankin Caribbean.

A ranar Asabar da ta gabata ne Donald Trump ya umarci ma’aikatar yaƙin Amurka da ta fara shirin ɗaukar mataki a kan Najeriya, inda ya gargadi gwamnati ta daina abin da ya kira kisan kiyashi ga Kiristoci.

Ya kuma bayyana Najeriya a matsayin “ƙasa ta ɓatattu.”

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi, inda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ƙasar tana mutunta ’yancin addini, kuma tana ɗaukar zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’umma a matsayin ginshiƙan haɗin kai na ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here