Da ɗumi-ɗumi: Gwamnatin tarayya ta fara biyan masu yiwa ƙasa hidima alawus na Naira dubu 77

NYSC Members 700x430

Gwamnatin tarayya ta fara biyan Naira dubu 77,000 alawus alawus na wata-wata ga masu yi wa kasa hidima (NYSC).

Sanarwar karin albashin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wanda tun da farko ya kawo jin dadi a tsakanin mambobin NYCS a fadin kasar nan, ya ci tura bayan jinkirin aiwatar da sabon alawus din.

Kusan watanni shida bayan sanarwar, ana ci gaba da biyan masu yi wa kasa hidima alawus alawus na N33,000 da aka gabatar a shekarar 2020 a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake tabbatar da wannan ci gaban ga SolaceBase a ranar Laraba, wata mai yiwa ƙasa hidima a jihar Kano, mai suna Nkiruka, ta ce an fara biyan su Naira 77,000, tana mai bayyana karin da cewa an dade ba a yi ba.

Ta ce mai yiyuwa ne ana biyan kudaden ne daki-daki, inda ta ce yayin da wasu ’yan NYSC A suka karbi nasu, wasu kuma na cikin zulumi.

Karin karatu: Babu tabbas ko zan tsaya takara a 2027 – Atiku

Har ila yau, wani mamban hukumar a Kano, Muhammad, ya bayyana farin cikinsa kan biyan sa sabon alawus din inda da ya bayyana a matsayin wani babban shiri.

Wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Ministan Cigaban Matasa Ayodele Olawande ya tabbatar wa ‘yan Najeriya hakan, yayin wata hira da gidan Talabijin na Channels cewa za a fara biya a karshen watan Maris.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here