Ban yi katsalandan a kwangilar wutar lantarki ta Mambilla ba, ba a kuma gurfanar da ni ba — Atiku ga APC

former Vice President Atiku Abubakar 750x430

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa kotun sasanta rikici ta Duniya (ICC) da ke Paris ba ta yanke masa hukuncin laifin cin hanci da rashawa ba a shari’ar da ta shafi kamfanin Sunrise Power da gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, babban mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin sadarwa, ya fitar a ranar Jumma’a, Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya ce ba ya cikin kwamitin saye da sayarwa da ya ba da kwangilar wutar lantarki ta Mambilla ga kamfanin Sunrise.

Wannan martani na Atiku ya zo ne biyo bayan kalaman kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na neman ya janye daga takarar shugaban kasa ta shekarar 2027 saboda zarginsa da lalata muradun Najeriya a kan wannan aiki na wutar lantarki.

Idan za a iya tunawa, a ranar Alhamis ne kotun ICC da ke Paris ta yanke hukunci goyon bayan Najeriya game da bukatar biyan diyyar dala biliyan 2.35 da kamfanin Sunrise Power ya nema a kan aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla.

Kotun ta yi watsi da ikirarin Sunrise na cewa Najeriya ta karya yarjejeniyar kwangilar da aka kulla da kuma karin bayanan da aka yi a kai.

Haka kuma, kotun ta umarci kamfanin Sunrise da Leno Adesanya, da su mayar wa Najeriya kudaden lauyoyi da suka kai dala miliyan 11.8.

Adesanya ya shaida wa kotun cewa dala 500,000 da ya tura wa Jennifer Douglas, wacce a lokacin matar Atiku ce, a watan Janairu 2003, wani bangare ne na mu’amalar musayar kudaden waje da ya yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa.

An biya kudin ne a ranar 30 ga Janairu, 2003, kasa da watanni hudu kafin a ce an bai wa Sunrise kwangilar don aikin wutar lantarki ta Mambilla, ta hanyar China Castle Investments Limited, wani kamfanin ketare da Adesanya ke iko da shi.

Bayanai kan wannan mu’amala da bayanin da Adesanya ya bayar suna kunshe ne a cikin hukuncin karshe da kotun ICC mai mambobi uku ta fitar a shari’ar da aka yi tsakanin Sunrise da Tarayyar Najeriya.

Da yake mayar da martani ga hukuncin kotun, kwamitin yakin neman zaben APC ya ce lokacin biyan kudin ya haifar da tambayoyi saboda an yi shi ne a lokacin tattaunawa kan aikin Mambilla.

Kwamitin ya yi zargin cewa Atiku, wanda ke zaman mataimakin shugaban kasa a lokacin, da Olu Agunloye, tsohon ministan wutar lantarki, sun hada baki don ganin an ba da kwangilar duk da rashin amincewar tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.

Yayin da yake mayar wa kwamitin martani, Atiku ya kalubalanci jam’iyyar APC da ta fito da “ainihin sashin da ke cikin hukuncin kotun inda ta gano cewa ya karbi rashawar dala 500,000, sannan ya umarci” Agunloye da ya ba Sunrise kwangilar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi kwamitin yakin neman zaben APC da laifin mayar da “zargi zuwa laifi, da kuma mu’amalar da ba a bayyana ba zuwa cin hanci da aka tabbatar”.

Atiku ya bayyana zargin kwamitin a matsayin “kagen siyasa”, inda ya kara da cewa APC na son maida “zargin da aka gabatar gaban alkalai ya koma hukuncin da alkalai da kansu ba su taba yanke shi ba”.

Atiku ya ce, “APC ba za ta iya kirkiro sakamakon binciken da babu shi ba kawai don ainihin hukuncin bai fito da sakamakon siyasar da take matukar bukata ba.”
“Najeriya ta yi zargi a gaban kotun cewa tura kudin yana da alaka da kwangilar Mambilla da ake takaddama a kai. Amma Sunrise da Adesanya sun musanta wannan zargi.

“Adesanya ya bayar da bayani wanda kotun ba ta amince da shi ba.

“Amma bayan da Leno Adesanya ya bayar wanda bai yi nasara ba baya zama hukuncin cin hanci da rashawa a kan Atiku Abubakar ba.

“Ban kasance mamba na tsarin fasaha da ya tantance shawarwari daban-daban ba kuma ya ba da shawarar Sunrise. Ban zauna a kwamitin sayayya ba.

“Ban bayar da kwangilar ba. Don haka duk wanda ke zargin cewa na yi katsalandan ga wannan tsari yana da alhaki mai sauki, ya nuna umarnin da na bayar, ya nuna katsalandan da na yi, kuma ya nuna sakin layi na hukuncin kotun inda aka gano wannan mummunan tasiri.

“Idan kotun na son ta gano cewa dala 500,000 cin hanci ne da aka biya Atiku, da ta fadi hakan a fili. Idan tana son ta gano cewa Atiku ya yi amfani da ofishinsa wajen neman kwangilar Sunrise, da ta fadi hakan a fili.

“Jam’iyyar APC ba za ta iya shigar da kalmomi da sakamako cikin hukuncin kotun sasanta rikici ta kasa da kasa wadanda alkalai da kansu ba su sanya su a ciki ba.”

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya kuma yi watsi da zargin cewa kotun ta neme shi amma ya yanke shawarar kin zuwa zaman kotun.

Atiku ya ce halartar tsoffin shugabannin kasa biyu — Olusegun Obasanjo da marigayi Muhammadu Buhari — a gaban kotun ba ya nufin cewa an neme shi da ya bayyana.

Atiku ya ce, “Domin kauce wa shakka, ni ban kasance daya daga cikin bangarorin shari’ar ba, kuma ban ba da shaida a gaban kotun ba.”

“Rahotannin abubuwan da ke cikin hukuncin ba su tabbatar da cewa kotun ta neme ni ba, ko ta umarce ni da in ba da shaida, ko kuma ta gano cewa na bijire wa wani umarni na bayyana ba.

Atiku ya kara da cewa a shari’arsa, masu zargin suna kokarin kirkiro zarge-zarge a kansa, ba kamar kwace dala 460,000 da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Amurka kan zargin alaka da miyagun kwayoyi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here