Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen jami’an hukumar tsaron Civil Defence (NSCDC) 21 da aka dakatar kan mutuwar mutane 37 da ake zargin masu hakar ma’adanai ne ba bisa ka’ida ba a hannun hukumar a Jihar Neja.
An dakatar da jami’an har sai an kammala bincike mai zaman kansa kan mutuwar da ta faru a ranar Alhamis, 17 ga Satumban 2026.
Read also: Tinubu zai kai ziyarar aiki Katsina ranar Juma’a – jami’i
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ce ta sanar da dakatarwar a cikin wata sanarwa da minister ya sanya wa hannu a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce dakatarwar ta biyo bayan kafa kwamitin bincike mai zaman kansa mai mambobi 10 don bincikar lamarin.
Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Jonathan Kure, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), yayin da Farfesa Isa Hayatu Chiroma (SAN), tsohon Darakta Janar na Makarantar Koyon Shari’a ta Najeriya, zai zama sakatare.
Sauran mambobin sun hada da AIG mai ritaya Hosea Hassan Karma, Farfesa Olayinka Buhari, Farfesar Histopathology tsohon Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin, wakilin Majalisar Masarautar Minna da wakilin Gwamnatin Jihar Neja.
Kwamitin ya kuma hada da Alhaji Liman Sulaiman, Sakataren Kasa na Kungiyar Masu Hakar Ma’adanai ta Najeriya, lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam Deji Adeyanju, Mrs Zainab Suleiman Okino ta Jaridar Blueprint da Dr George Agbakahi, manazarci kan harkokin jama’a.
An bai wa kwamitin makonni biyu don kammala aikinsa tare da gabatar da rahotonsa ga ministan.
A cewar sanarwar, ana sa ran kwamitin zai gano sahihan mutanen da suka mutu tare da bincikar kamasu, tsare su da kuma musabbabi da yanayin mutuwarsu.
Ministan ya kuma umurci kwamitin da ya gano alhaki, ciki, sakaci da kuma mummunan aiki, tare da bayar da shawarar matakin da ya dace da kuma diyya inda ta dace.
An dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, a baya.
Sauran jami’an NSCDC 20 da aka dakatar sune:
O/C Station Guard, SC Usman Isah Ndamaka
Station Guard, ASCI Hassan Mohammed
Station Guard, CCA Bala Mohammed
Jami’in Kame/O/C Bincike, CSC Oluwadare Sunday
Read also: Gidan yarin Goron Dutse ya yi bikin cika shekaru 100 da fara gudanar da aiki a Kano
Jami’in Kame, DCC Obafemi Elvis
Jami’in Kame, CSC Annas Shitto Lamino
HOD INT/INV, DCC Philip Ajayi
O/C Legal, ACC Barr. Stephen Tsado
Jami’in Aikin Dare, ASCI Alhassan Mohammed
Jami’in Tsaro, IC Abdullahi Sale
Jami’in Tsaro, IC Mohammed Sonfada
Jami’in Tsaro, CAI Liman Abubakar
Jami’in Tsaro, CAI Bala Usman
Jami’in Tsaro, IC Mohammed Jiya
Jami’in Tsaro, DSC Isah Suleiman
Jami’in Tsaro, CAI Ahmed Wushishi
Jami’in Tsaro, IC Sale Adamu
Jami’in Tsaro, IC Haruna Mohammed
Jami’in Tsaro, ASCI Aliyu Sallah
Read also: Kotun koli ta tabbatar da Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan Zamfara
Jami’in Tsaro, CAI Isah Sanusi
Ministan ya mika ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da yin kira da a kwantar da hankali yayin da ake ci gaba da bincike.










































