An samu karancin fitowar masu zabe a ranar Asabar, yayin zaben cike gurbin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ke gudanarwa a mazabar Dawakin Kudu ta jihar Kano.
Wakilan kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) da suke sanya ido kan aikin sun bayar da rahoton cewa an samu isasshen tsaro a dukkan rumfunan zabe da suka ziyarta.
Read also: CBN ya maida martani kan rahotannin shirin soke lasisin bankunan Unity da Keystone da Polaris
NAN ta ruwaito cewa jam’iyyun siyasa shida ne a zaben da suka hada da ADP, APP, APC, LP, PDP da PRP suks tsayar da ‘yan takara.
Ta kuma ruwaito cewa jami’an INEC sun isa mafi yawan rumfunan zabe kafin karfe 8 na safe, kuma an samar da kayayyakin zabe a kan lokaci.
NAN ta kara da cewa a duk rumfunan zaben da aka ziyarta, an gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali, yayin da masu zabe suka tsara kansu cikin lumana.
Wasu daga cikin rumfunan zaben da aka ziyarta sun hada da 021, 022, da 03 a mazabar Dawaki da kuma 037, 020, da 017 a mazabar Kofar Yamma.
Read also: Ya kamata a dage babban taron APC zuwa wani lokaci- ‘ya’yan APC na Burtaniya
A halin yanzu, wasu masu zaben da suka zanta da NAN sun bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da zaen tare da yabawa INEC kan gudanar da aiki cikin sauki.
A cewar Mustapha Abdullahi, mai zabe, zaben cike gurbin na daga cikin zabe mafi kwanciyar hankali da aka gudanar a yankin a baya baya nan.
Ya yaba da tsare-tsaren da INEC ta sanya da kuma yadda jami’ai suka gudanar da aikin.
Sai dai Abdullahi ya danganta karancin fitowar da yanayin zaben, yana mai cewa a al’ada zaben cike gurbi na mazabar jiha baya jawo yawan fitowar masu zabe.
Read also: Trade | Khám phá Thế giới Giải trí Trực tuyến với Kubet 77 – Hướng dẫn và Kinh nghiệm chơi | 5-2025
Hakazalika, Aisha Hamisu, wata mai zabe, ta ce sun zo rumfar zaben ne don zaben dan takarar da suke goyon baya.
Ta ce suna fatan dan takararsu zai lashe zaben kuma ya cika alkawuran da ya yi musu.(NAN)












































