Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Sanata Abdul Ahmad Ningi na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Bauchi ta tsakiya.
Abdul Ningi ya samu kuri’u dubu 104 da 878 inda ya samu nasara akan babban abokin hamayyarsa Uba Ahmed Nana na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u dubu 84 da 621.
Jami’in dake tattara sakamakon zaɓen Farfesa Ibrahim Danjuma, ne ya bayyana sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zaɓen dake Darazo a karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi.
Haka kuma, Sanata Isah Hamma na jam’iyyar NNPP shi ne ya kasance na uku a zaɓen inda ya samu kuri’u dubu 17 da 995.












































