A gaggauce: Tinubu ya umarci a janye dukkanin ƴan sandan da suke ba da tsaro ga mutane na musamman

President Bola Tinubu 1 1 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a janye dukkan jami’an ‘yan sanda da ke bayar da tsaro ga mutane na musamman a faɗin ƙasar nan domin su koma gudanar da muhimman ayyukan su na yau da kullum.

Wannan na nufin daga yanzu hukumomin ‘yan sanda za su mayar da waɗannan jami’ai kan ainihin ayyukan tsaron da aka ɗora musu, domin ƙara inganta tsaro a yankunan da ake fama da ƙarancin jami’ai.

Umarnin na zuwa ne jim kadan bayan kammala taro kan sha’anin tsaro da shugaban ƙasa ya jagoranta a Abuja tare da shugabannin rundunar sojin sama, rundunar sojin ƙasa, hukumar tsaron cikin gida ta ƙasa, da sufeto janar na ‘yan sanda.

Daga cikin abin da umarnin ya ƙunsa akwai cewa duk wani mutum na musamman da ke buƙatar kariya daga jami’ai zai nemi waɗanda aka tsara su daga hukumar tsaron na Civil Depence.

A wasu yankunan ƙasar, musamman wajen da suke da nisa, rashin isassun jami’an ‘yan sanda a ofisoshi na kawo cikas wajen kare fararen hula da dukiyoyinsu daga barazanar tsaro.

Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: Tinubu na taron gaggawa da Hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaba Tinubu ya ce ana ɗaukar matakai domin ƙara yawan jami’an ‘yan sanda a ƙasa baki ɗaya, inda ya amince da ɗaukar ƙarin jami’ai 30,000 tare da haɗa kai da jihohi wurin inganta cibiyoyin horo.

Taron ya samu halartar manyan hafsoshin tsaro ciki har da Laftanar Janar Waidi Shaibu, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, sufeto janar Kayode Egbetokun da daraktan hukumar tsaro ta DSS Tosin Adeola Ajayi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here