Sarkin Zazzau, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna, mai martaba Amb. Ahmad Nuhu Bamalli, ya naɗa Muhammad Inuwa Aminu, a matsayin sabon Wazirin Zazzau.
Rahoton Solacebase ya ruwaito cewa, Muhammad Inuwa Aminu, ya kasance tsohon sakataren jaridar New Nigerian, haka kuma Alkali a kotun daukaka kara ta shari’ar musulunci.
Bayanin nadin na kunshe ne cikin wasika mai dauke da kwanan wata 11 ga watan Oktoban 2021, wadda Alhaji Barau Musa Aliyu, sakataren masarautar Zazzau ya aikewa sabon Wazirin.
Wasiƙar ta bayyana cewa, nadin ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar Kaduna ta bayar cikin wata wasika zuwa ga masarautar, mai dauke da kwanan wata 20 ga watan Satumban, 2021.
Ta kara da cewa, nadin ya fara aiki ne nan take daga ranar Litinin, 11 ga watan Oktoban 2021.













































