Budaddiyar wasika zuwa ga shugaban kasa MUHAMMADU BUHARI, Kwamandan askarawa.

President Buhari sad sad
President Buhari sad sad

Mai Girma Shugaban kasa,

Muhammadu Buhari, GCFR.
kuma babban kwamandan askarawa.

Abuja,

Yallabai,

Muna rokon ka da kayiwa alummar kasa jawabi kan kwamitin da ka kafa a sirran ce dan bincike da kwato kudaden bugun hatimi cikin gaggawa.

Taron gamayyar kungiyoyin fararen hula na jahohi goma sha tara na Arewacin Najeriya da Abuja.

Ranka ya dade, muna yi maka barka da sabuwar shekara, kuma muna taya ka murna kan rattaba hannu kan dokar kasafin kudi na shekarar 2023, aikin da ya kasance na karshe a wa’adin mulkin ka ga ‘yan Najeriya.

Yallabai, muna so ka waiwayo da hankalinka kan batun da ke yawo a Nijeriya dangane da wani kwamitin da aka ce ka kafa a boye a karkashin ikonka, domin ya binciki zargin badakalar harajin tambarin Naira Tiriliyan 89.

Mu a matsayinmu na ‘yan kungiyoyi da ke aiki a jihohin Arewa goma sha tara da abuja, mun damu matuka da irin makudan kudade da aka ce wasu ’yan tsiraru ne suke amfani da su. Ayayin da ake samun wawan gibi akasafin kudi duk shekara kuma ake dogara kakokan a rance.

Yallabai, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a jihar Jigawa, ya yi ikirarin cewa kun kafa kwamitin sirri na shugaban kasa, karkashin jagorancin wani Mista Adetola Adekoya. don bincika kudaden shiga harajin hatimi da aka daɗe.

A ra’ayinmu masu nazari, zai zama babban illa ga al’umma, idan a matsayinka na Babban Kwamandan askarawan Najeriya, ka ci gaba da yin shiru kan wannan batu na kasa, wanda ba kawai ya dauki hankulan ‘yan Najeriya ba ne, har da kuma al’ummomin duniya.

Ranka ya dade, daya daga cikin maganganu masu daukar hankali kan wannan tirka tirka shine cewa “Nigeria ƙasa ce da gwamnati ke karɓar kuɗin gwamnati kuma tana ba da kudin ruwa ga wasu tsirarun mutane” tabbas wannan batu na bukatar karin haskakawa. don kawar da kai tamkar tozarta martabar gwamnatin ku ce, kamar yadda wasu jami’an Gwamnati suka yi ta nuna yatsa a cikin wannan dambarwa, tare da ceton martabar kasarmu mai daraja, wadda a halin yanzu ke tangal tangal da hadari.

Sa hannu:

Shugabannin gamayyar kungiyoyi na arewacin Najeriya da Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here