An tsaurara matakan tsaro a Adamawa gabanin ziyarar shugaba Buhari

Nigeria Police Constable Recruitment
Nigeria Police Constable Recruitment

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, ta girke ƙarin jami’an tsaro domin tabbatar da komai ya tafi daidai gabanin ziyarar shugaba Buhari a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, shi ya tabbatar wa manema labarai hakan a Yola yau Asabar.

Ya ce sun bukaci jami’an da su nuna ƙwarewa da kuma mutunta ‘yancin dan adam yayin gudanar da aiki.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Buhari zai ziyarci jihar ne a ranar Litinin domin kaddamar da ƴakin neman zaɓen ‘yar takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Binani.

Kakakin ‘yan sandan ya ce ƙarin jami’ai da girke sun haɗar da rundunonin jami’an tsaro da jami’an sashin ƴaki da ta’addanci da kuma motocin samame.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here