Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu maza biyu

FB IMG 16730864547758430
FB IMG 16730864547758430

Iran ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu maza biyu saboda zarginsu da kashe wani jami’in tsaro yayin zanga-zangar gama-garin da aka shafe sama da wata uku ana yi a ƙasar.

Mahukunta a ɓangaren shari’a sun bayyana sunan mutanen da Mehdi Karami mai shekara 22 da Seyyed Mohd Hosseini, mai shekara 20.

Dukkansu dai an same su ne da hannu a mutuwar jami’in tsaron sa kan a birnin Karaj kusa da Tehran.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here