Sama da mutum 37 ’yan bindiga suka sace a hare-haren da suka kai wasu kauyukan Jihar Kaduna a cikin kwana ukun da suka gabata.
Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Azara da Janjala da kuma Kadara, cikin kananan hukumomin Kagarko da Kachia a jihar.
Jaridar Aminiya ta gano galibin wadanda lamarin ya shafa mata ne, ciki har da masu shayarwa da kuma kananan yara.
Yayin hare-haren, ’yan bindigar sun kashe wani tsohon soja da dansa a kauyen Katambi da ke makwabtala da garin Kateri.
Ya ce kafin su kai ga sanar da sojojin da ke sintiri a yankin abin da ke faruwa, ’yan ta’addar sun riga sun tsere.
Rugar Alhaji Karbo da kauyen Kurutu da wani kauyen Kadara da Janjala a Kagarko da sauransu, na daga yankunan da hare-haren ta’addancin suka hana wa barci ido rufe in ji majiyarmu.













































