Kamata yayi Atiku ya rage kudin makarantar sa in har da gaske yana kishin ilimi – Kwankwaso

L R Rabiu Kwankwaso and Atiku Abubakar
L R Rabiu Kwankwaso and Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP Sen. Rabi’u kwankwaso yace kamata yayi Atiku, Dan takarar PDP ya rage kudin makaranta a jami’ar sa ta Amurka dake Najeriya, idan har da gaske yake ” inji Rabiu Kwankwaso.

Kwankwaso wanda tsohon gwamnan Kano ne kuma dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka a zauren taron na daren jiya, inda yace Mista Abubakar zai iya yin kyau idan ya rage kudin makarantar.

“Matakin da Abubakar ya dauka na kafa jami’a a matsayin hanyar taimakawa ilimin Najeriya ya yi “kyau”, in ji Mista Kwankwaso a taron da aka nuna a gidan talabijin na Arise TV.

“Dole in gode wa Wazirin adamawa, yana da jami’a, jami’a wanda abu ne mai kyau,” in ji Mista Kwankwaso. “Abin da kawai ya kamata shi ne ya yi ƙoƙari ya rage kudin makarantar don ‘yan Najeriya da yawa su iya shiga jami’ar.”

Duk da cewa ba a bai wa Atiku Abubakar damar mayar da martani ga kalaman na Kwankwaso ba, sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce kalaman abokin hamayyar nasa ya saba wa ka’idojin muhawarar, wadda ga dukkan alamu hakan bai yiwa atiku dadi ba.

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Rabi’u Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na jam’iyyar Labour na daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa dasuka halarci tattaunawar ta yau, yayin da Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ya fice daga zauren taron, wanda ya zo sa’o’i bayan ya tashi zuwa London bisa gayyata daga Chatham House

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here