Tsohon Shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya musanta zargin da ake yi masa cewa akwai hannunsa dumu dumu cikin rikicin da ya addabi jam’iyyar PDP a ƙasar nan.
Rahotanni sun ce Gwamnonin jiha biyar ne a yanzu suka ja tinga da ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kuma suka haƙiƙance cewa sai shugabanta na ƙasa Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa zasu janye makaman su.
Cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafofin yaɗa labarai, Ikechukwu Eze ya fitar, Jonathan ya musanta zargin da ake yi cewa da sa hannunsa a rikicin.
“Mun samu labari maras tushe da ake yaɗawa cewa gwamnonin da ke rikici da jam’iyya sun bayyana goyon bayansu ga Dr Goodluck Jonathan,” a cewar sanarwar. “Da mun ga dama za mu iya yin shiru gameda wannan tirka tirka saboda abin ba shi da wani tushe.
“Sai dai muna wannan bayani ne saboda da yawa daga ‘yan Najeriya sun nemi jin bahasi daga gare mu tare da nuna damuwar mu kan wannan tankiya.”
Gwamnonin da ake yi wa laƙabi da G5 masu rigima da ɓangaren Atiku su ne: Nyesom Wike na Ribas, da Seyi Makinde na Oyo, da Okezie Ikpeazu na Abiya, da Samuel Ortom na Binuwai, da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.













































