Za a daina karbar Dalar kudi da aka buga kasa da shekarar 2021, farawa daga 31 Jinairu 2023.

Naira, Dala, CBN, BDC, sayar, karyata
Sabanin rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta na Facebook da X (Twitter) da ke ikirarin cewa ana musayar Dalar Amurka tsakanin Naira 900 zuwa...

Biyo bayan kwarya-kwaryan taron da aka kammala a birnin Washington DC na Amurka a ranar 2 ga Nuwamba, 2022 tsakanin Babban Bankin Tarayya na Amurka, Ofishin Kwanturolar Kudi, Asusun bada lamuni, Bankin Duniya da Gwamnonin Manyan Bankunan Afirka, gwamnatin Amurka ta tsayar da ranar dena karbar takardar kudin Dalar Amurka musamman tsaffi dasuka jima da bugawa wanda zai fara a ranar 31 ga Janairu, 2023.

Gangamin taron ya fidda matsaya cewa za a dena karbar Dalar amurka baki daya wadanda aka buga su ƙasa da shekarar 2021 a ko’ina a fadin duniya.

Rahotanni sun ce wannan yunkurin dai wani mataki ne na dakile biliyoyin kudaden da aka tara ba bisa ka’ida ba cikin samfurin kudaden daloli da aka taskace a sassan nahiyar Afirka wadanda keda alaka da kudaden muggan kwayoyi, ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma kudaden sata daga gurbatattun ‘yan siyasa.

Hakanan an ce yayin fara aiwatar da wannan mataki akwai tsauraran matakai da shirin da za a bawa manyan bankunan Afirka tare da tura wakilai na musamman daga Ofishin Kwanturolar Kuɗi na Bankin Ƙasar Amurka don bincikar duk wani shige da ficen daloli.

Rahoton ya kuma bayyana cewa Shugaban Amurka Joe Biden ya kuma rubutawa gwamnatin Birtaniya da kungiyar Tarayyar Turai da su ma su sake fasalin kudadensu yadda ya kamata domin murkushe tareda maganin wadanda suka wawashi kudaden da ba su dace ba na dalar Amurka da Fan Sterling da kuma Yuro.

Jaridar Solacebase ta samu labarin cewa za a aiwatar da wannan matakin ne a watan Janairun 2023, yayin da ‘Yan siyasar Najeriya dasu kayi kaurin suna a fagen cin hanci da rashawa zasu ji a jikin su, kamar yadda sanarwar ta nuna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here