Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 Asiwaju Bola Tinubu ya ce nasarorin da ya samu a matsayinsa na gwamnan jihar Legas za su iya maimaituwa a Najeriya idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Tinubu ya bayyana haka ne a farkon Jawaban da ya gabatar na yakin neman zaben sa wanda aka kaddamar a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da takardar mai shafi 80 a hukumance tare da jiga-jigan jam’iyyar da manyan jami’an gwamnati a dakin taro na Banquet Hall dake Abuja.
Tinubu ya ce a shirye ya ke ya maimaita irin bajintar da ya yi na tsawon shekaru takwas a jihar Legas a fannin daban daban dan sauya fasalin kasar.
A cikin Jawabin nasa mai shafuka 20, dan takarar shugaban kasa ya lissafa tsarin kiwon lafiya, ilimi da samar da gidaje a matsayin muhimman wuraren da zai fi mayar da hankali.
”Abin da ni da tawagara muka cimma a Legas, tabbas tare duk za mu iya sake maimaita makamancin sa a Najeriya.












































