Rahotanni daga birnin fatakwal sun ce Ofishin yakin Neman zaben dan takarar Shugaban kasa na jamiyyar PDP atiku wbubwkar a jihar ribas ya kasance a kulle adaidai lokacin da ake cigaba da gudanar da yakin neman zabe.
Rufe ofishin nada alaka da umarnin da gwamnatin jihar ribas karkashin Gwamna Woke ya bayar na garkame ofishin.
Rahotanni sun ce ofishin na rukunin unguwar fitattun mutane ta GRA dake birnin fatakwal.
Gwamna wike a makonnin da ya gabata ya rattaba hannu kan dokar hana bude ofishin yakin Neman zabe ba tareda Neman izinin gwamnati ba
Dayake maida martani, kakakin kwamitin yakin neman zaben Dan takarar PDP a jihar yace sun nemi amincewar gwamnatin tsawon makonni, saidai a tsawon lokutan gwamnatin ba tace musu komai ba.
Idan za a iya tunawa, Gwamna Wike na takun-saka da Atiku abubakar tun bayan lashe tikitin takarar kujerar Shugaban kasa a jamiyyar PDP lamarin da ya janyo Gwamnan yin taware tareda bujire duk wani aikace aikace dake da alaka da takarar atiku abubakar.
Gwamna Wike cikin bukatun sa, na neman a sauke Shugaban jamiyyar da ya fito daga jihar benuwe tareda bukatar maida kujerar shiyyar kudancin kasar nan.













































