Jam’iyyar APC ta bayyana dalilan da suka sanya aka cire sunan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo cikin jerin sunayen kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima.
Jaridar Solacebase ta ba da labarin cewa sakin sunayen wadanda aka nada a cikin jerin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa bai hada da Yemi Osinbajo ba wanda hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin jama’a.
Cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a kuma babban mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Festus Keyamo ya rawaito cewa karamin ministan kwadago ya ce shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin cewa mataimakin shugaban kasa da kuma Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha bai kamata a sanya su su cikin kwamitin yakin neman zaben ba, abu mafi dacewa su cigaba da tafiyar da mulkin kasa.
Idan za a iya tunawa, Yemi Osinbajo ya fafata ne a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC tare da Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar a zaben 2023 da ya lashe zaben fidda gwani azubuka mai zuwa.












































