Gwamnatin tarayya zata fara aikin titin daya tashi daga Numan zuwa Jalingo akan kudi naira biliyan 3

BUHARI signs 1
BUHARI signs 1

Gwamnatin tarayya ta amince da aikin gina titin da ya tashi daga Numan zuwa Jalingo wanda zai lakume naira biliyan uku 3.

Karamin ministan ayyuka da gidaje, Injiniya Mu’azu Sambo Jaji ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar duba ayyukan da ake yi a ciki da wajen jihohin Taraba da Adamawa.

Ya ce Aikin titin Numan zuwa Jalingo zai lashe Naira biliyan uku, kuma wani bangaare ne na daga cikin aikin babban hanyar Maiduguri zuwa Calabar.
Ya ce za a biya dan kwangilar da zai yi aikin a watan Yuli domin fara aikin, inda kumaa ake sa ran kammala aiki akan lokacin da aka tsara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here