Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta amince da dokar kafa hukumar tsare-tsare da habaka tattalin arziki

Kano State House of Assembly 700x430

Majalisar Dokokin Jihar Kano a ranar Litinin ta amince da kudurin dokar da ke neman kafa Hukumar Tsare-tsare da Habaka Tattalin Arziki ta Jihar Kano.

An amince da dokar ne bayan nazari da karbar rahoton da Kwamitin daukacin mambobin majalisar ya gabatar a kan kudurin.

Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawal Hussaini, mai wakiltar karamar hukumar Dala, ya bayyana cewa hukumar tana da alhakin daidaita ayyuka a tsakanin kananan hukumomi da gwamnatin jiha domin habaka yanayin tattalin arzikin jihar.

Ya bayyana cewa gwamnan jiha ne zai jagoranci hukumar, yayin da mambobinta za su hada da Kwamishinojin Kasafi da Tsare-tsare, na Kudi, na Ilimi da na Shari’a, gami da shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar.

Hussaini ya kara da cewa za a hada da fitattun mutane guda biyar masana fannoni daban-daban a matsayin mambobi domin bayar da tasu gudunmawar wajen inganta tattalin arzikin jihar.

Ya kara da cewa Ma’aikatar Al’amuran Kananan Hukumomi ta jihar ce za ta samar da sakatariyar gudanarwa ga hukumar idan an kafa ta.

“Manufar wannan dokar ita ce tsara shirye-shiryen ci gaban tattalin arzikin jihar.

“Haka kuma za ta daidaita ayyuka a tsakanin majalisun kananan hukumomi da jiha domin kawo ci gaban tattalin arziƙi a jihar.”
Wannan dokar tana neman kafa hukumar ne karkashin sashi na 7(3) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da sauran al’amuran da suka shafi hakan.
Haka zalika, dan majalisa mai wakiltar Ghari da Tsanyawa, Garba Ya’u-Gwarmai, ya yi kira ga majalisar da ta matsa wa gwamnatin jiha lamba domin mayar da darasin Kimiyyar Na’ura mai kwalƙwali ya zama dole a makarantun jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da duk kayayyakakin da suka dace domin saukaka koyo da koyarwar darasin yadda ya kamata a makarantun firamare, sakandare da manyan makarantun gaba da sakandare na jihar.

A gefe guda kuma, Shugaban Majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya karanta wasikar da ta fito daga hannun Gwamna Abba Kabir-Yusuf, yana neman amincewar majalisar kan nadin mutane biyu a matsayin mambobin Hukumar Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano.

Mutanen da aka zaba sun hada da Hajiya Uwani Bello Makama da Alhaji Ahmad Auwalu Ibrahim.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here