’Yan Sanda sun ceto mutane 75 da aka yi garkuwa da su a Kaduna

IMG 9361 750x430

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta ceto mutane 75 da aka yi garkuwa da su da suka hada da maza, mata da yara, wadanda wasu ’yan bindiga suka sace a kauyen Folwaya da ke kusa da Birnin Gwari.

An ce wadanda aka sace Fulani ne matafiya, kuma an sace su ne a ranar Laraba yayin da suke cikin motocin haya.

Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ‘Yan Sanda, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 5:30 na yamma a ranar 19 ga Agusta, 2026, bayan samun bayani daga reshen kungiyar direbobin motoci ta kasa NURTW na Birnin Gwari.

A cewarsa, wasu ’yan bindiga ne da ba a san ko su waye ba dauke da bindigogi kirar AK-47 da sauran manyan makamai, suka sace su tare da tasa su cikin daji.

Ya ce masu garkuwar daga baya sun boye wadanda aka sace a cikin wani rami a wani yanki mai duwatsu.

Hassan ya ce bayan sun samu bayanin, tawagar ’yan sanda ta musamman daga Hedikwatar Birnin Gwari ta tashi zuwa wurin nan take.

Ya kara da cewa zuwan ’yan sandan ya sa ’yan bindigar suka gudu suka bar wadanda aka sace, inda aka ceto su lafiya ba tare da wani rauni ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yaba wa reshen NURTW na Birnin Gwari saboda bayanan da suka ba su cikin gaggawa wanda ya taimaka wajen ceto mutanen.

Haka kuma ya yaba wa Kwamandan Yankin Birnin Gwari da jami’ansa bisa gaggawar da suka yi da kuma kwarewar da suka nuna.

CP ya roki al’umma da su ci gaba da lura da kewayensu tare da kai rahoton duk wani motsi ko aikin da basu amince da shi ba.

Duk da haka, ya gargadi jama’a da kada su dauki doka a hannu, yana mai cewa hakan na iya sa rayukan marasa laifi cikin hadari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here