Ranar Matasa ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 12 ga Agusta na kowace shekara, bai kamata ta kasance kawai ranar jawabai, biki da shagali da sanarwar gwamnati na yaba kokari, kirkire-kirkire da juriyar matasa ba.
Ya kamata ta zama lokaci da Najeriya za ta yi wa kanta tambaya mai wuya, idan gaskiya ne matasa ne shugabannin gobe, to wane lokaci ne ainihin wannan gobe zata zo?
Wannan tambaya tana da matukar muhimmanci a Najeriya saboda kasar tana da yawan matasa sosai. A cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa NPC, sama da kashi 60 cikin 100 na ‘yan Najeriya suna kasa da shekaru 30.
Asusun Majalisar Dinkin Duniya na Yawan Jama’a UNFPA ma ya ce kashi 63 cikin 100 na ‘yan Najeriya suna kasa da shekaru 25. Wannan ya sanya Najeriya cikin kasashen da suka fi kowanne yawan matasa, wanda ke baiwa kasar babba dama tare da nauyi mai girma.
Taken Ranar ta bana shi ne “Mabambantan Yanayi, Buruka Iri Daya”. Yana nufin duk da cewa matasa suna rayuwa cikin yanayi daban-daban, suna da buri guda na mutunci, shiga cikin al’amura, samun dama da kyakkyawar gobe.
Amma a Najeriya, batun ba kawai yin murnar kan fatan da ake yi wa matasan. Tambayar ita ce: Shin kasar tana shirya su da sosai don su gaji nauyin siyasa, tattalin arziki da zamantakewa? Ko kuma kalmar “shugabannin gobe” ta zama ta fatar baki kawai da ake maimaitawa daga tsara zuwa tsara?
Tarihin Najeriya ya bamu wani darasi daga mai kyau.
A da can, ana bai wa matasa damar yiwa kasa aiki suna da kananan shekaru.
Misali, Janar Yakubu Gowon ya zama Shugaban Kasa a 1966 yana da shekaru 31. Janar Murtala Muhammed ya zama shugaba a 1975 yana 36. Janar Olusegun Obasanjo ya hau mulki a 1976 yana kusan 38, yayin da Janar Muhammadu Buhari ya zama shugaba a Disamba 1983 yana 41 sai kuma Janar Ibrahim Babangida ya hau mulki a 1985 yana 44.
Wannan ba gangamin goyon bayan dawo da mulkin soja ba ne, Najeriya ta sha wahala da mulkin soja. Amma abin da muke nufi shi ne a da an dauki matasan Najeriya a matsayin masu iya daukar nauyin kasa, yayin da yanzu tsarin siyasar mu ke ganin matasa a matsayin marasa kwarewa.
Al’amarin lura a yanzu shi ne, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, an haife shi a 1952, yana da shekaru 74. Tsohon Mataimakin Shugaba Atiku Abubakar, an haife shi 1946, yana 79. Tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana 76. Rabiu Musa Kwankwaso yana 69. Sanata Kabir Gaya yana 74, Sanata Rufai Sani Hanga yana 72.
Tinubu ya zama Sanata yana 38, sannan Gwamna yana 47 a 1999. Atiku ya tsaya takar gwamna yana 44. Kwankwaso ya zama Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai yana 34, sannan Gwamna yana 43. Kabir Gaya ma ya zama gwamna yana 38.
Babu matsala idan tsofaffi sun ci gaba da hidima. Kwarewa tana da amfani. Amma matsalar ta taso ne lokacin da siyasa ta zama sana’a ta dindin maimakon nauyi da za a mika wa tsara na gaba.
Ba za mu iya ci gaba da gaya wa kashi 60 cikin 100 na al’ummar da suke kasa da 30 su ci gaba da jiran goben da masu mulki ba su shirya musu ba.
Matsalar ita ce, ana ba matasa damar zabe amma ba a ba su damar mulki ba. Ana amfani da su a gangamin siyasa, buga fasta, yin fadan siyasa, kare ‘yan siyasa a shafukan sada zumunta da jefa kuri’a. Amma lokacin da ake yanke shawara, ba a basu damar zama a cikin dakin.
An hana matasa dama a siyasa, aiki, kasuwanci, ilimi da yanke shawara. Yawancinsu suna da kuzari amma babu jari, babu ilimi mai kyau, babu dama ta siyasa. Wannan ya haifar da takaici, dogaro da bacin rai.
Kuma mu matasan mu duba kanmu, Shin mun shirya da gaske don mu hau mukaman da muke nema?
Kasancewa matashi ba ya nufin kai shugaba na gari ba ne. Dan siyasa mai shekaru 30 da ke cin hanci bai fi dan siyasa mai shekaru 70 mai gaskiya ba. Matashi marar ilimi da ladabi ba zai iya ba da jagoranci mai kyau ba saboda kawai yana matashi.
Kuma muna da matsalar da ba za mu iya musantawa ba shan miyagun kwayoyi, yahoo, cult, daba a siyasa, sata da zamba. ‘Yan siyasa na amfani da wasu matasa a matsayin makamai. Wasu sun shiga ayyukan laifi saboda rashin aikin yi da rashin kyakyawan fata.
Amma kada mu yanke wa dukan tsara hukunci. Yawancin matasan Najeriya masu aiki ne, dalibai, ‘yan kasuwa, manoma, ‘yan jarida, masu sana’a da kirkire-kirkire.
Me za a yi? Jam’iyyun siyasa su bude hanya ta gaske ga matasa su tsaya takara, ba kawai kirkirar youth wing don kamfen ba, sannan gwamnati ta saka jari a bangaren ilimi, sana’a, fasaha da aikin yi.
Haka zalika, tsofaffi su fahimci cewa babban gado shi ne shirya masu maye shi, ba zama a a kujera har abada ba. Matasa mu daina barin a yi amfani da mu. Mu nemi ilimi, mu guji miyagun kwayoyi, mu shiga siyasa a matsayin masu ilimi, ba taron haya ba.
Najeriya ba ta bukatar kawai canja tsofaffi da matasa ba. Tana bukatar canja al’adun siyasa daga son kai zuwa cancanta, daga rashin lissafi zuwa amana, daga amfani da matasa zuwa ba su dama ta gaske.
Lokaci ya yi da za mu daina cewa matasan Najeriya “shugabannin gobe ne”. Su ‘yan kasa ne na yau, kuma dole ne a ba su dama su ba da gudummawa yanzu, yayin da suke shirin jagorantar gaba.
Tsofaffi su ba da dama. Matasa su shirya kansu. Jam’iyyu su bude kofa. Gwamnati ta samar da dama. Kuma matasa kada su bada gobensu ga miyagun kwayoyi, laifi da neman arziki cikin sauki.
Lokacin shirya matasan Najeriya na gobe ba gobe ba ne. YANZU ne lokacin.













































