Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kama karin mutane uku da ake zargi da hannu a sace Shugaban Tsangayar Aikin Gona na Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Samuel Avengbe Okunsebor.
An kama mutane ukun ne a daren ranar Jumma’a a wani gidan karuwai da ke kusa da Mararraban Akunza, a kan babban titin Lafia zuwa Makurdi, kamar yadda wata majiyar tsaro da ke da masaniya kan binciken lamarin ta bayyana.
Wannan ci gaba ya zo ne bayan da jami’an DSS suka ceto Okunsebor kwanaki biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi da sanyin safiyar ranar Laraba, 15 ga Yuli 2026, a Mile Uku, wata unguwa da ke kan iyaka tsakanin Lafia da kananan hukumomin Nasarawa-Eggon.
Haka kuma, jami’an na DSS sun kama mutane biyu da ake zargi, ciki har da mace guda, a daidai lokacin da aka ceto malamin.
Yayin da yake ba da cikakken bayani game da sabbin kamun da aka yi, majiyar tsaron ta ce an gano sunayen mutane ukun da aka kama, Yakubu Abubakar mai shekaru 25, wanda aka fi sani da Black/Starboy, Usman Abubakar Mairiga mai shekaru 37 da Sale Babauro Abubakar mai shekaru 27.
Ya ce, “An gano wadanda ake zargin wato Yakubu Abubakar Black/Starboy dan shekara 25, dan kabilar Doemak a jihar Plateau, Usman Abubakar Mairiga dan shekara 37 da kuma Sale Babauro Abubakar dan shekara 27.”
Majiyar ta kara da cewa Mairiga Bahaushe ne, yayin da Sale Babauro Abubakar bafullatani ne.
A cewar majiyar, rundunar shiyar jihar tana tsare da mutane ukun domin ci gaba da gudanar da bincike.
Majiyar ta ce, “Wadanda ake zargin suna tsare a hannun rundunar jihar domin gudanar da bincike na gaba,” sannan ta kara da cewa tsare su ya biyo bayan “samun ingantaccen sammacin tsarewa daga kotun majistare.”
An yi garkuwa da Okunsebor ne a Mile Uku, da ke tsakanin Lafia da Nasarawa-Eggon, kafin jami’an DSS su ceto shi kwanaki biyu bayan haka.
Sabbin kamun da aka yi ya samar da adadin mutanen da aka kama dangane da lamarin zuwa biyar, kodayake ba a bayyana sunayen mutane biyu da aka kama da tun da fari ba a cikin bayanan da aka fitar.













































