Zaben Osun: EFCC ta kulle asusun Gwamnatin Jihar Osun

EFCC Osun

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), ta kulle wani asusun Gwamnatin Jihar Osun na First Bank, kwanaki 10 kafin zaben gwamna.

An ce ana amfani da asusun wajen biyan albashin ma’aikatan gwamnati, kuma hukumar yaki da cin hanci ta sanya shi a matsayin (Post No Debit) wato ba za a iya cire kudi gada cikin shi ba.

Wannan lamari ya faru ne sa’o’i kadan bayan Gwamna Ademola Adeleke ya zargi EFCC da shirin kulle asusun gwamnatin jihar da na manyan jami’an gwamnati.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kai, Kolapo Alimi, ya fitar a ranar Laraba, gwamnan ya bayyana wannan mataki da aka ruwaito a matsayin kokarin kawo cikas ga ayyukan gwamnati gabanin zaben gwamna na ranar 15 ga Agusta.

Adeleke ya ce babu wata hujja ta doka da za ta baiwa EFCC damar kulle asusun gwamnatin jihar, yana mai cewa hukumar ba ta da ikon daukar irin wannan mataki.

Wata majiya da ke kusa da gwamnan da ta bukaci a sakaya sunanta saboda ba a ba ta izinin yin magana ba, ta ce an riga an kulle asusun.

“Zan iya tabbatar muku cewa EFCC ta kulle asusun gwamnatin jihar. Ba zargi ba ne kuma. Gwamna zai gana da manema labarai nan ba da jimawa ba don sanar da jama’a halin da ake ciki,” in ji majiyar.

Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here