Yajin Aiki: Majalisar Dattawa ta fara sulhunta tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya

Senate 1 750x430

Majalisar dattawa ta fara matakan sulhu tsakanin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU, da gwamnatin tarayya, domin kawo karshen yajin aikin gargadi na makonni biyu da malaman ke gudanarwa.

Kwamitocin majalisar dattawa kan kwadago, cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare, da asusun raya jami’o’i (TETFUND) za su gana da ministan ilimi, Malam Tunji Alausa, da sakataren hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa (NUC), Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu, a mako mai zuwa.

Wannan taro zai biyo bayan ganawar da kwamitocin majalisar suka yi yau da shugabannin kungiyar ASUU a majalisar, inda suka tattauna kan hanyoyin warware rikicin.

Shugaban kwamitin kan jami’o’i da TETFUND, Sanata Muntari Dandutse daga Katsina ta Kudu, ya bayyana cewa sun saurari korafe-korafen ASUU kuma majalisar za ta tura matsalolin zuwa ga hukumomin da suka dace domin neman mafita.

Majalisar ta kuma bayyana cewa za ta gana da ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, domin dakatar da duk wani yunkuri na kwace filayen jami’ar Abuja da ake zargi da faruwa.

A baya kafin rufe ganawar, shugaban ƙasa na kungiyar ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, ya bayyana cewa babban matsalar ita ce rashin cikakken aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta cimma da su, wadda ta shafi batun kudaden raya jami’o’i.

Ya ce rashin zuba jari mai dorewa a bangaren ilimi ne ke sa yajin aiki ya zama ruwan dare a jami’o’in kasar.

Farfesan ya ƙara da cewa duk da majalisar ta amince da naira biliyan 150 don jami’o’i, sai biliyan 50 kawai aka fitar zuwa ma’aikatar ilimi, inda ake zargin ana shirin raba kudin ga sauran cibiyoyi kamar kwalejoji da makarantu na fasaha, duk da cewa kowanne yana da nasa kasafin kudi.

Majalisar dattawa ta tabbatar da cewa za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da an sasanta bangarorin, domin gujewa yajin aikin da ka iya zama na dogon lokaci a jami’o’in kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here