Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Kasa (INEC), ta ki amincewa da takardar neman takarar Shugaban Kasa ta tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da tsagin PDP karkashin jagorancin Kabiru Turaki ya gabatar.
Tun da farko, a ranar Juma’a tsagin Turaki sun dage cewa sun mika takarar Jonathan da sunayen sauran ‘yan takararsu na zaben 2027 ga hukumar ta hanyar takardu, wanda ya kara dagula rikicin jagoranci a jam’iyyar.
Darakta mai kula da wayar da kai da yada labarai na INEC, Victoria Eta-Messi, ta shaida wa Saturday Vanguard cewa hukumar ba ta amince da mika takardu a wajen dandalin yanar gizo da ta tanada ba.
“Mika takardu ana yi ne kawai ta wani dandali na musamman kamar yadda ka’idoji da jagororinmu suka tanada,” in ji ta.
Amma Sakataren Yada Labarai na tsagin Turaki, Kwamared Ini Ememobong, ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin ya zabi mika sunayen ta hanyar takardu ne bayan INEC ta ki ba su lambobin turawa da ake bukata wajen aikewa ta yanar gizo. Ya ce lambobin suna ne kawai don sauwake aiki ba wani sharadi na doka ba.
“Ba tare da la’akari da hanawar INEC ba na lambobin da ake bukata… mun yi nasarar mika jerin sunayen ‘yan takararr da Jam’iyyar PDP ta gaskiya ta zaba, ta hanyar takardu bisa cikakken bin Dokar Zabe ta 2026,” in ji Ememobong













































