Wata tawaga ta musamman ta ‘yan kasuwan Kano da manyan jami’an gwamnati ta gana da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, domin neman a gaggauta sakin kudin tallafin rage radadi Naira biliyan 5 da Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin bayarwa ga wadanda gobara ta shafa a Kasuwar Singer.
Wannan na cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, tawagar ta tunatar da Gwamnatin Tarayya alkawarin da ta yi a farkon wannan shekarar na tallafawa dubban ‘yan kasuwa da gobara ta lalata musu harkokinsu da hanyoyin samun abin rayuwa.
Sanarwar ta jaddada cewa gaggauta sakin kudin agajin zai samar da mafita ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa, sannan zai hanzarta dawo da harkokin kasuwanci a kasuwar.
A lokacin ganawar, tawagar ta bayyana godiyarta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da tallafin, sannan ta roki a kammala matakai domin masu cin gajiyar su samu tallafin ba tare da wani jinkiri ba.
SolaceBase ta ruwaito cewa cikin tawagar akwai Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwar Kano, Alhaji Sabiu Bako, Kwamishinan Kudi, Dr. Ismail Aliyu Danmaraya, Hon. Muhammad Jamu Yusuf, Shugaban Kasuwar Singer Barrista Junaidu Muhammad Zakari da dan kasuwa Alhaji Kabiru Adamu Gano.
Sakataren ya tabbatar wa tawagar cewa ya lura da kokensu, sannan ya sake jaddada kudurin Gwamnatin Tarayya na tallafawa wadanda gobara ta shafa a Kasuwar Singer.













































