Rushewar gini: Masu tsara gine-gine sun bukaci a tsaurara matakai da tilasta ka’idojin gini

Building collapsed file 750x430

Damuwa na ci gaba da karuwa kan ci gaba da samun lamarin rushewar gine-gine, Kungiyar Masu Tsara Gine-gine ta kasa (NIA) reshen jihar Kano ta bukaci a tsaurara matakin tilasta bin ka’idojin gini.

Shugaban kungiyar, Mustapha Mukhtar ne ya yi wannan kiran yayin da ya jagoranci tawaga daga kungiyar zuwa wurin da wani gini ya rushe kwanan nan a kan Titin Sultan, Karamar Hukumar Nassarawa, Kano, domin duba halin da ake ciki.

Cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar, Salim Bashir Abdullahi ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa Shugaban ya ce dole ne a tilasta bin ka’idojin gini a kan ayyukan gwamnati da masu zaman kansu domin hana sake faruwar irin wannan lamari.

Mukhtar, wanda ya nuna damuwarsa kan lamarin rushewar ginin, ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano, Majalisar Rijistar Masu Tsara Gine-gine ta Kasa (ARCON) da sauran hukumomin da ke kula da harkokin gini su tabbatar cewa ana daukan kwarru kuma masu rijista kawai a ayyukan gini.

“Bayan duba wurin, tawagar ta lura da cewa babu wata alama da ke nuna cewa an dauki kwararrun masana gini masu rijista a wannan aikin.

Babu allon nuni da ana aiki a kan titunan da ke kaiwa wurin ko a wurin, kuma babu matakan tsaro a wurin kamar shingen wucin gadi.
“Kungiyar ta ce rashin kulawar kwararru da ake gani ya jawo babban damuwa kan bin ka’idojin gini na doka da kuma ka’idojin harkar.”

A cewarsa, ci gaba da faruwar rushewar gine-gine lamari ne da ya shafi jama’a baki daya.
“Tilasta bin ka’idojin yadda ya kamata da kuma daukar kwararrun masana masu rijista abubuwa ne da suka zama wajibi domin kare rayuka, dukiya da kuma tabbatar da amincewar jama’a kan harkar gini.”

Mukhtar ya kara jaddada cewa masu gine-gine da sauran kwararru masu rijista a fannin gini kamar Injiniyoyi, Masu Kiyasin Kudin Gini da sauransu suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa an tsara gine-gine yadda ya kamata, kula da su, sanya ido, kuma an aiwatar da su bisa ka’idoji da dokoki.

Shugaban, wanda ya mika ta’aziyyarsa ga wadanda lamarin ya shafa, ya sake jaddada kudurin kungiyar na yin aiki tare da hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta harkar, tsaron jama’a da ci gaba mai dorewa a fadin jihar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here